Jami’an kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da su rika yin amfani da mazauna gari idan za a yi aikin rigakafi a Najeriya.
Jami’in kiwon lafiya Paul Bassi ya yi wannan kira a Abuja a taron da kungiyar DRPC da kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya NACHPN suka shirya domin samar da hanyoyin bunkasa yin allurar rigakafi a Najeriya.
Bassi ya bayyana cewa yin amfani da mazauna gari zai sa a iya samun daman yi wa yara da yawa rigakafin sannan zai ba damar iya shiga duk wani kurdi domin ganin an cimma buri.
” Misali a lokacin da muke jihar Bauchi mun sami sauki da nasarar yi wa yara allurar rigakafi fiye da yadda muka yi zato saboda mun yi amfani da wanzamai.
” Wanzaman da muke tare da su a wannan lokaci sun nuna mana yara da gidajen da za mu shiga don yi musu allura. Da ya ke sune suke yi musu kaciya sun raka zuwa gidajen da yara suke muna ta yi musu allura.