Jam’in ma’aikatar lafiya dake Abuja Humphrey Okoroukwu ya bayyana cewa cutar kwalara ta bullo a wasu gundumomi dake garin Abuja sannan an rasa rayukan mutane 7 zuwa yanzu.
Ya fadi haka ne a Abuja da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.
Ya ce cutar ta kashe mutane biyu a kauyen garin Kubwa, mutum daya ya mutu a Sauka, biyu a unguwar Mpape sannan da biyu garin Ushafa
Okoroukwu ya ce cutar ta fi yaduwa a garin Ushafa sai dai ba a rasa rai ko daya ba a kauyukan Kwali da Kuje.
A karshe ya yi kira ga mutane da su mai da hankali wajen tsaftace muhallin su da kuma gaggauta garzayawa asibiti idan ba aji dadin jiki ba. Sannan gwamnati ta wadata babban asibiti dake karamar hukumar Bwari da magani domin tunkarar wannan cuta.
Discussion about this post