WHO za ta bada gudunmawar maganin rigakafin zazzabin shawara a Najeriya

0

Jami’ar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar WHO za ta ba Najeriya gudunmawar maganin allurar rigakafi zazzabin shawara har na miliyan 12 a shekarar 2018 sannan ta kara bada magani na miliyan 19 a 2019.

Charity ta bayyana haka ne a Abuja inda ta kara da cewa WHO za ta samar da wannan gudunmawa ne da hadin guiwar Kamfanin GAVI.

A wani rahoton hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) zazzabin shawara ta bullo a kananan hukumomi 22 a kasar nan, sannan mutane 4200 sun kamu kuma 47 sun rasu cikin su.

Charity ta ce suna kokarin ganin an kau da wannan zazzabi zuwa 2026.

Za a far yin allurar ne daga ra 8 zuwa 18 ga watan Nuwamba, a jihohin Sokoto, Kebbi, Neja, Filato, Barno da babban birnin tarayya Abuja.

Share.

game da Author