Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi tofin Allah-tsine dangane yadda aka bari sai a ranar jajibirin taro, aka hana Rabiu Kwankwaso yin amfani da Dandalin Eagle Square domin ya kaddamar da neman takarar shugaban kasa a zaben 2019.
A cikin wani bayani da Kakakin Yada Labaran Saraki, Yusuph Olaniyonu ya sa wa hannu, Saraki ya ce, “Dandalin Eagle Square na kowane dan Najeriya ne.”
Ya kara da cewa soke amincewar da aka yi wa Kwankwaso yin amfani da filin, ya tabbatar da yadda a karkashin wannan gwamnatin dimokradiyya ke tafiyar-kura.
“Wannan Dandali na Eagle Square dai na kowane dan Najeriya ne, domin da kudin Najeriya aka gina shi ba da kudin wani ba. Mu na fatan ba irin wannan rashin adalcin za mu rika ci gaba da gani ba, ganin cewa mu na kara kusantar zaben 2019.” Haka aka ruwaito Saraki ya fada.
Gwamnatin Buhari, musamman shi kan sa shugaban Kasa ya na ci gaba da shan suka ganin yadda aka bada dalilin cewa an hana Kwankwaso yin taron ne saboda ya zo daidai da ranar aiki.
Daga nan sai ‘yan adawa suka tuna wa Buhari yadda shi ma yay i nasa taron kaddamar da takarar sa ta 2015, a filin Eagle Square, kuma a ranar Laraba, alhali shugaban lokacin Goodluck Jonathan bai hana shi ba.
Discussion about this post