Jami’an ‘Yan sandan kasar Saudiyya sun kawo samame karkashin wasu gadoji dake birnin Makka, inda Tukaru ke siyar da abinci a boye.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya shugaban hukumar Alhazai ta Kasa Abdullahi Mohammed ya gargadi Alhazan Najeriya da su nesanta kan su daga siyan abincin irin wadannan mutane.
” Bincike ya nuna cewa wadannan mutane a dakunan bahaya suke dafa abincin.” Inji Abdullahi.
A Bidiyon da ya iske mu zaka ga mata da yara suna guje-guje dauke da komatsen su suna arce wa a daidai ‘yan sandan sun kawo musu samame.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=9cvKMuPW9BY&w=560&h=315]