Firayi Ministar Birtaniya Theresa May, ta isa Fadar Shugaba Muhammadu Buhari domin ganawa da shi nan ba da dadewa ba.
Ta isa a cikin wata mota samfurin SUV, mai lamba 138 CMD da misalin karfe daya na rana, kuma Shugaba Buhari ne ya tarbe ta, tare da wasu jami’an gwamnati.
Ta dauki hotuna da Buhari, sannan kuma daga nan suka shiga cikin ofishin sa da misalin karfe 1:06 na rana.
Wannan ce ziyarar ta ta farko, daga cikin rangadin da ta ke yi a kasashen Afrika a matsayin ta na Firayi Minista.
Kafin zuwan ta Najeriya, ta isa Afrika ta Kudu jiya Talata inda ta gana da shugaba Cyrill Ramaphosa.