Kakakin tsohon gwaman jihar Kaduna, Ramalan Yero, Ahmed Maiyaki ya bayyana cewa lallai lokaci ya yi da mutanen Kaduna zasu hada karfi da karfe, a tattaru waje daya, kowa ya daura kambun sa, masu jigida duk a daura domin kauda Gwaman jihar Nasir El-Rufai daga kan karagar mulki a 2019.
Maiyaki ya bayyana haka ne da ya ke zantawa da wasu wakilan jam’iyyar PDP da suka kawo masa ziyarar barka da sallah a gidan sa dake Kaduna.
” Sanin kowa ne cewa lokaci yayi a taru a hada kai domin a tabbata gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai bai zarce a wannan kujera na gwamna ba.
” Jihar Kaduna ta zama abin tausayi yanzu rashin zaman lafiya yayi wa jihar Katutu, Masu Garkuwa da mutane sun addabi jihar, Barayin shanu, ga kuma kashe-kashe a kullum, baya ga bakin talauci da mutanen jihar Ke fama da shi.
” Shiga Kaduna yanzu ya zama tashin hankali. Mutane da dama kan soke zuwa garin Kaduna saboda tsoron rashin zaman lafiya da ya addabi jihar.
” Kowa a jihar yanzu yana zaman dar-dar ne domin baka san dame gwamnatin jihar zata fafureka ba. Ko dai a sallame ka a aiki ne , ko a rusa maka gida ko kuma a saida gidan da kake ciki haka kawai.
A bisa wadannan dalilai ne ya sa nake kira ga dukkan mai son ci gaban jihar Kaduna da ya zo mu hada hannu mu ceto jihar mu daga hannun irin wannan mulki.
Ahmed Maiyaki na tare da dantakar gwamnan jihar Kaduna Sani Sidi, tsohon shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA sannan fitaccen dan jarida ne.

” Muna sane da nukufarcin da ake shirya wa sannan da karerayin da ake yi game da takarar maigirma Sani Sidi, wannan ba zai sa mu karaya ba, za mu ci gaba da bin jama’a domin ganin ya samu nasarar zama dan takarar gwamnan a inuwar Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Discussion about this post