WHO ta yi kira ga kasashen Afrika su maida hankali wajen dakile yaduwar cututtuka

0

Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira ga shugabanin kasashen Afrika da su maida hankulan su wajen dakile yaduwar cututtuka da ke addabar mutanen Nahiyar.

Cututtukan da ake kamuwa dasu kai tsaye ko kuma ake gado kamar su Hawan jini, shanyewan jiki, ciwon siga, da makamatan su na daga cikin wadanda aka zayyano domin a maida hankali matuka wajen samar wa mutanen nahiyar Kariya da magani.

Jami’ar kungiyar WHO Rebecca Moeti ta yi kira ga shugabanin kasashen Afrika da su maida hankali wajen hana yaduwar ire-iren wadannan cututtuka a kasashen su.

Ta zayyano wasu hanyoyi da za a iya kamuwa da wadannan cututtuka da suka hada da canjin yanayi, gado, rashin cin abincin dake bunkasa karfin garkuwar jikin da sauran su.

Bayan haka ta ce bincike ya nuna akalla kashi 30 bisa 100 na mutanen nahiyar Afrika na fama da ire-iren wadannan cututtuka.

A karshe ministan Lafiya na Najeriya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta tashi tsayin daka domin ganin ta kakkabe yaduwa da samar da mafita ga masu dauke da wadannan cututtuka.

” A yanzu haka mun hada hannu da WHO don tsara hanyoyin kula da masu fama da hawan jini a jihohin Yobe da Ogun sannan muna kokarin kafa dokar hana siyar da taba a kasar domin ceto lafiyar mutane.”

Share.

game da Author