Ministocin Yankin Tafkin Chadi na taron neman mafita a Abuja

0

Ministocin kasashen da ke makwabtaka da Yankin Tafkin Chadi na taron neman mafita da shawo kan matsalolin da ke tattare da yankin, musamman rikicin Boko Haram.

Ana ganawa ne domin neman mafita daga matsalolin tattalin arzikin kasa da ya dabaibaye yankin, musamman har da batun kafewar Tafkin Chadi.

Taron na neman yadda za bi ko a dauki matakan farfado da tattalin arzikin yankin wanda Boko Haram ya yi wa raga-raga.

Ana taron ne tsakanin ministocin, masana da kuma wakilan Shirin Farfado da Tattalin Arziki na Majlisar Dinkin Duniya.

Haka Shugaban Hukumar Farfado da Tafkin Chadi, Mamman Nuhu ya shaida a wurin taron a Abuja, wanda ke gudana o Otal din Hilton.

Taron wanda za a shafe kwanaki uku ana yi, za a tattauna hanyoyi 9 ne da nufin cimma wannan babbar manufa.

Share.

game da Author