Mawallafin jaridar PREMIUM TIMES Dapo Olorunyomi ya yi kira ga kafafen yada Labarai na kasar nan da su na yayada nasarorin da gwamnatin Najeriya ke yi musamman wadanda suka shafi kiwon lafiyar mutane domin kaucewa ci gaba da yaduwar cututtuka musamman cutar kanjamau da ake fama da shi.
Ya fadi haka ne a wani taron sanin makaman aiki da tattauna matsalolin da ake fama da su musamman wadanda suka shafi cutar Kanjamau wanda gidauniyar ‘AIDS Healthcare Foundation’ ta shirya a Abuja ranar Litini.
Olorunyomi ya bayyan cewa bayanai sun nuna cewa kashi 95 bisa 100 na kudaden da ake amfani da su don yaki da cutar kanjamau a Najeriya tallafi ne da ake samu daga gwamnatin kasar Amurka da sauran kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje.
” Duk da yawan kudade na tallafi da ake samu a kasar nan babu dalilin da zai sa a wayi gari ace har yanzu ana samun karancin magani da kuma yawan yaduwar cutar kanjamau a Najeriya.”
” Wannan babban dalili ne da dole kafafen yada labarai su maida hankali wajen binciko inda wadannan kudade ke tafiya da kan sa ake fadawa cikin wadannan matsaloli.
A karshe shugaban hukumar (NACA) Sani Aliyu ya bayyana cewa lallai wannan matsala da ake fama da su na ci wa gwamnati tuwo a kwarya, sannan dole ne a maido da hankula kacokan bisa wannan matsala da ake fama da su a zage damtse domin an kai ga ci a abin da aka sa a gaba, Sannan yayi kira ga gwamnatocin jihohi da su maida hankali a kai.