Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya, ta bayyana cewa ta na shirye-shiryen gyara wasu gine-gine na gwamnati da maharan da suka addabi jihar Zamfara suka lalata wasu yankunan jihar.
Daraktan Riko na Sashen Yada Labarai na Hedikwatar, John Agim ya ambaci haka a Gusau, jiya Juma’a.
Burgediya Janar Agim, ya bayyana wa manema labarai a Gusau cewa ayyukan da sojojin za su gudanar sun hada gina rijiyon burtsate, gyaran ajjuwan makarantun da suka lalace da kuma dakunan ganin likita ko na shan magani a yankunan da rikice-rikice suka shafa.
Ya kara da cewa kuma sojojin a su gudanar da ayyukan duba lafiya da bayar da magana a cikin karkarar da mahara suka yi barna.
Ya ce a lokaci guda kuma za a inganta matakan tsaro a cikin yankunan.
Ya jaddada cewa sojojin ‘Operation Sharan Daji’ na ci gaba da gudanar da shirin kakkabe mahara a cikin nasara a duk lokacin da suka nausa gaba ko suka kai farmaki a kan ‘yan ta’addan.
“Mu na samun nasarar kwato dabbobi, muggan makamai da ma wadanda maharan ke yin garkuwa da su.