Kimanin mata 200 su ka amfana daga tallafin kudade na kai-tsaye daga Gidauniyar Aisha Buhari, Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, a jihar Katsina.
Kakakin yada labaran Aisha, Suleiman Haruna, ya bayyana a cikin wata takardar da ya raba wa manema labarai.
An gudanar da taron a Babban Dakin Taro na Multi Purposes, Katsina.
Taron ya samu halartar dandazon mata wadanda su ke gudanar da kananan sana’o’i, musamman tasarifin amfanin gona sa sana’o’i na tireda da sauran saye da sayarwa daban daban.
Akwai masu saida kosai, waina, kayan shafe-shafa, dinki da saka.
Kodinatan Gidauniyar Aisha Buhari, Kamal Muhammad, wanda shi ne ya wakilci Aisha, ya ce kudadden talafin wadanda ake turawa kai tsaye a cikin asusun ajiyar matan a bankin su, an kirkiro shi ne domin inganta lafiya da rayuwar mata da kananan yara.
Ya kara da cewa wannan shiri da kuma tsarin tallafi zai inganta sana’o’in matan ta hanyar samun karin riba da kuma kudaden shiga.
Daga nan sai ya kara da cewa zai inganta ilmin yara, lafiyar iyali da sauran matakan da ake son cimma musamman a shirin muradun karni.
Kwamishinar Ilmi ta Jihar Katsian, Badiyya Mashi, ta gode wa uwargidan shugaban kasa a bisa jajircewar ta a ko da yaushe wajen inganta rayuwar mata ta hanyar tallafa wa sana’o’in su, domin su rika dogaro da kan su.
Discussion about this post