‘Yan sanda sun gayyaci tsohon Ministan Sufurin Jirage, Femi Fani-Kayode, dangane da zargin wani rubutu da yay i da suka ce zai iya tunzura barkewar rikici.
Dama kuma Fani-Kayode, wanda rikakken dan adawar gwamnatin Buhari ne, ya na fuskantar hukumar warure kudade.
Ya saba caccakar gwamnatin Buhari a cikin soshiyal midiya. Sai dai kuma zuwa yanzu ba a san abin da ya rubuta wanda jami’an tsaro ke ganin zai iya haddasa barkewar rikici.
Kwamishina Habu Sani da ke sashen sa-ido a kan laifuka ne ya sa wa takardar neman Fani-Kayode hannu.
Sun ce ana neman Kayode da ya bayyana a gaban sufurtabda Usman Garba, domin amsa wasu tambayoyi.
An ce ya kai kan sa a ranar 28 Ga Agusta, 2018.
Discussion about this post