Rashin yin bincike kan sabbin magunguna na kawo wa Kasa ci baya

0

Wani farfesa da ya kware a harkar binciken magunguna dake aiki a jami’ar Obafemi Awolowo mai suna Joseph Aladesanmi ya koka kan yadda gwamnati bata ware isassun kudade domin gudanar da bincike a kasar nan ba.

Aladesanmi ya ce rashin ware isassun kudade da gwamnati ke yi na hana wa Najeriya ci gaban da ya kama ce ta.

“Sanin kowa ne cewa Najeriya itace kasar da ta fi kowace kasa a yankin Afrika daraja amma ci gaban dake wasu kasashen Afrika ya fi na Najeriya.

“Hakan na da nasaba ne da rashin mai da hankali da gwamnatin kasar ke yi wajen rashin ware kudade domin gudanar da binciken da zai kawo wa kasar ci gaba mai amfani.

Aladeanmi da shine ya gano sabuwar maganin cutar daji mai suna ‘Acuminatoside’ ya bayyana cewa ya gudanar da binciken wannan magani ne duk da kudi daga aljihunsa sannan har yanzu gwamnati ta ki cika alkawarin biyan sa duk kudaden da ya kashe.

Ya ce duk wadannan na cikin kalubalanen dake kawo wa Najeriya koma baya a musamman ayyukan ci gaba da ta sa a gaba.

Share.

game da Author