Zainab ta haifi ‘ya’ya hudu a sansanin Maradun

0

A yau Litini ne wata ‘yar gudun hijira dake samun mafaka a sansanin Maradun dake jihar Zamfara mai suna Zainab Salisu ta haifi ‘ya’ya har hudu.

Zainab da mijin ta Salisu Muhammad mazauna kauyen Gidan Dan-Guntu ne dake karamar hukumar Maradun da ta yi fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Zainab dai ta haifi ‘ya’ya hudu, mata biyu maza biyu a ranar Lahadi da taimakon wata ungozoma dake tare da su a sansanin.

Mahaifin jariran Salisu ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litini cewa Zainab sau daya ta je asibiti awon ciki tun da ta same shi.

Wani Likita da ke aiki a asibitin Yariman Bakura dake Gusau da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa NAN cewa Zainab da ‘ya’yan ta hudu na cikin koshin lafiya sannan kawo su asibitin da aka yi da wuri ya taimaka matuka.

Share.

game da Author