Jagoran Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zayyano wasu dalilai da ya sa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal suka fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
A wata takarda da ya saka wa hannu da kan sa Tinubu ya ce babban dalilin da ya sa Saraki da Tambuwal suka fice daga APC shine don su cimma burin su na siyasa da ke kokarin fin karfin su muddun za su ci gaba da zama a jam’iyyar APC.
” Sauran ‘yan siyasar kuma duk sun koma PDP ne domin basu samun abin da suke nema ba wato a raba kudaden jama’a su handame su.
” Shi Tambuwal buri ce ta cika shi fam. So yake ya nemi takarar shugabancin Najeriya. Amma kuma Buhari yayi masa katangar karfe tsakanin sa da wannan kujera. Shi ne ya lallaba ya tattauna da gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike, inda ya yi masa alkawarin za a bashi tikitin takara a PDP idan ya sauya sheka.
” Bayan haka kuma wani abu da ya kara tada masa da hankali shi ne alamu da ya gani cewa kujerar gwamna ma da ya ke kai sai ya yi takarar fidda gwani da sauran ‘yan takara a APC.
” Idan ba don gwamna Wike ya yi masa alkawarin zama dan takarar PDP ba ina ganin da bai fice daga APC ba.” Inji Tinubu
” Shi ko Saraki ta sa tayi kama da ta Tambuwal domin shima shugabancin Najeriya yake so, amma Buhari yayi masa Katangar karfe.
Idan har yace zai fito takara to zasu gwabza da su Tambuwal kenan. Sai dai ya shinshino hakan, sai yake neman goyon bayan yan PDP din da ko ta halin kaka ya iya dawowa majalisa a matsayin shugaban ta.
Tinubu ya ce sauran ‘yan siyasan da suka fice kuwa duk kwashi kwaraf ne masu neman ko ta halin kaka a raba kudin kasa maimakon ayi wa mutane aiki da su.
Discussion about this post