Mutumin da dan sa ya rasu sanadiyyar azabtarwar SARS ya nemi hakkin sa

0

Wani mutum mai suna Hassan Abdullahi, ya nemi rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bi umarnin kotu ta hanyar biyan diyyar naira miliyan 10 da kotu ta umarci ‘yan sanda su biya, sanadiyyar mutuwar da dan sa ya yi a hannun jami’an SARS, saboda azabtarwa.

Abdullahi ya shaida wa Sashen Hausa na BBC a yau Labara, yadda dan karamin rashin jituwa tsakanin Hassan da ‘yar uwar sa ya kai su ofishin ‘yan sanda a Kano.

Abdullahi ya yi ikirarin cewa yayin da aka je ofishin ‘yan sanda, sai SARS suka maida rashin jituwar zuwa zargin fashi da makami, daga nan suka rika gallaza wa Hassan har hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa.

A hirar da aka yi tsakanin Abdullahi da wakilin BBC, ya ce sabani aka samu tsakanin Hassan da ‘yar uwar sa, daga nan sai ta kai shi kara ofishin ‘yan sanda.

“Amma a ofishin ‘yan sanda, sai suka ce min wai ‘yan fashi da makami ne, kuma aka dauke su zuwa ofishin SARS, inda dan nawa Hassan ya sha azaba a hannun su.

“A wannan daren sai SARS suka kira ni, suka ce min wai da na ya na ta aman jinni. Na garzaya can da safe, amma na samu da na ba ya ma iya magana. Daga nan sai suka amince su bayar da belin sa. Na garzaya da shi asibiti, inda a can ya rasu.” Inji Abdullahi.

“Daga nan sai na kai kara a Babbar Kotun Kano. Kotu ta yanke hukuncin cewa su biya ni diyyar naira milyan 10, amma har yau ba su biya ba. Kuma tun cikin 2015 aka yanke hukuncin.”

“Yan sanda sun daukaka kara, aka kira ni sau daya kawai, daga nan shari’ar ta mutu.”

Abdullahi ya bayyana wa BBC cewa a lokacin Hassan ya samu karo karatu a Jami’ar Eagypt kafin mutuwar ta sa.

“Yanzu haka ma ina nan tare da takardar daukar sa jami’ar da kuma bizar shirin tafiyar sa Egypt din. Tun daga abin da SARS suka yi wa da na, har yau ban koma daidai cikin hayyaci na ba.

Da aka tambaye shi dangane da umarnin da Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bayar na a yi wa SARS garambawul, sai Abdullahi ya ce, duk wani canji in dai canjin suna ne kawai, “ai zancen banza ne.”

Share.

game da Author