Kungiyar Kiristoci, CAN za su yi wa Najeriya azaumi da addu’ar kwana uku

0

Kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN, ta bayyana cewa Kiristoci za su yi wa Najeriya azumi da addu’o’in kwanaki uku a daukacin coci-cocin fadin kasar nan.

Kungiyar ta bayyana cewa za su gudanar da azumin da addu’o’in a ranakun 27 da 29 ga Agusta, domin neman ubangiji ya kara tsarkake kasar nan da kuma tsare dimokradiyyar ta.

Shugaban CAN na Kasa, Samson Ayokunle ne ya yi wannan sanarwar a cikin wani jawabi da mataimakin sa na musamman a fannin yada labarai da sadarwa, Adebayo Oladeji ya sa ka wa hannu.

Ayokunle ya ce azumin da addu’o’in sun zama tilas ganin yadda asarkalar siyasa ke wa dimokradiyyar Najeriya shiga hanci da kudundune, wanda shugaban na CAN ya ce barazana ce da turbar dimokradiyyar kasar nan.

Daga nan sai ya umarci dukkan shugabannin kiristoci na shiyyoyi, jihohi da kananan hukumomi na coci-cocin kasar nan gaba daya da su tattara mambobin cocin su domin su yi shirin azumin da kuma addu’o’in.

“Wadannan addu’o’i da azumi za su kara wa kiristoci kaimin kusantuwa ga ubangijin su a wannan lokaci na gabatowar zaben 2019.” Inji Shugaban CAN.

Share.

game da Author