Likitocin Abuja za su fara yajin aiki

0

Kungiyar likitoci reshen babban birnin tarayya Abuja (ARD) ta sanar cewa ta ba hukumar gudanarwa na babban birnin tarayya wa’adin kwanaki 21 ko kuma ta shiga yajin aiki idan har gwamnati bata biya mata bukatun ta ba.

Hakan ya biyo bayan wata takardar da shugaban kungiyar Michael Olarewaju da sakataren kungiyar Roland Aigboyo suka saka wa hannu cewa zasu fara yajin aikin.

Kungiyar ta bayyana cewa baza ta amince da cire Naira 78,000 din da aka yi daga albashin su na watan Yuli a matsayin wai haraji ba.

” An tursasa mana mu rika biyan Naira 36,000 daga cikin albashin mu na kowani wata amma sai gashi an cire mana Naira 78,000 daga albashin watan Yuli saboda haka muna bukata a biya mu kudaden mu tunda wuri.”

Shugaban kungiyar Michael Olarewaju ya ce sun gono haka ne a binciken da suka gudanar a hukumar karban harji na babban birnin tarayya Abuja inda suka gano cewa cire Naira 78,000 da akayi daga albashin su baya cikin doka.

Ya ce dokar ta bada damar a cire Naira 36,000 ba Naira 78,000 bane.

Olarewaju yace a dalilin haka ne suka ba gwamnati wa’adin kwanaki 21 daga ranar 3 zuwa 25 ga watan Agusta.

Sun gargadi ministan Abuja Muhammed Bello da ya saurare su tun da wuri ya dau mataki a kai ko su shiga yajin aikin.

Sauran bukatun kungiyar sun hada da biyan alawus din kwanaki 28 na kowani wata wanda gwamnati ta ki biya tun a shakarar 2011 da kara wa likitocin da suka ci jarabawar karin girman da aka yi tun a shekarar 2016 girma da biyan su albashin yadda ya kamata.

Share.

game da Author