GARGADI: Harsken wayan kira na makantar da mutum– Bincike

0

Wasu likitoci daga jami’ar Toledo a kasar Amurka sun gargadi mutane da su guji amfani da wayar tarho a cikin rana da duhu domin hasken na iya makantar da mutum.

Shugaban likitocin Ajith Karunarathne ya bayyana haka inda ya kara da cewa hakannya yiwu ne bayan wani bincike da suka gudanar.

” Binciken da muka gudanar ya nuna cewa harsken dake fitowa daga waya da ake kira Blue Light na iya kashe jijiyoyin da suke taimaka wa ido wurin ganin haske da sauran abubuwa da ake kira Photoreceptors da turanci.

Karunarathne ya ce binciken ya kuma kara nuna musu cewa hasken na daya daga cikin abubuwan dake sa mutane a kasar Amurka kamuwa da cutar makanta.

A karshe yace domin guje wa irin haka ne suke kira ga mutane da su rika amfani da tabarau ko kuma maganin da zai taimaka wajen rage kafin hasken waya yibwa idanu illa.

Share.

game da Author