A yau Litini ne hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa ta samar wa ‘yan gudun hijira 29,000 dake zaune a sansanonin dake karamar hukumar Anka kayan tallafi.
Jami’in hukumar na shiyyar Sokoto Sulaiman Mohammed ya sanar da haka wa kamfanin dillancin labaran Najeriya inda ya kara da cewa NEMA ta ciko manyan motoci hudu dankare da kayan abinci,tufafi da kayan da za su tsaftce jiki da muhali domin tallafa wa mazauna sansanonin dake Anka.
” A gobe Talata ne mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai ziyarci jihar. Bayan haka zai ziyarci karamar hukumar Talatan Mafara.
Mohammed ya hori mazauna sansanonin da su yi amfani da kayan agajin yadda ya kamata sannan ya jinjina wa sarkin Anka Attahiru Ahmad bisa ga namijin kokarin da yayi wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin masarautar sa.