’Yan sandan Abuja sun bindige ’yar bautar kasa

0

‘Yar uwar wata ‘yar bautar kasa, ta fito karara ta zargi ‘yan sandan Najeriya da laifin kashe ‘yar uwar ta.

Ta ce sun harbe Nkechi Igwetu ne a daidai inda ska shingen bincike kan titi.

Chinenye Igwetu ta ce an dirka wa ‘yar uwar ta bindiga ne a jiya Laraba da safe, a lokaci da ta ke faiya a cikin mota tare da wasu abokan ta masa da nufin zuwa wurin wata dina.

Da ya ke ba a gaban Chinenye aka kashe ‘yar uwar ta Nkechi ba, ta ce an yi harbin ne a Central Area kusa da Ceddi Plaza.

Nkechi ta rasu a daidai lokacin da aka isa asibiti da ita. Vdama kuma an harbe ta ne wajen karfe uku na dare.

Ta ce abokan yar uwar ta ne suka ba ta labarin duk yadda abin ya faru, kuma da ta je ofishin ‘yan sanda suka kara yi mata bayani.

An rika watsa hotunan Nkechi a soshiyal midiya ana zargin cewa ma’aikatan asibitin Garki, Abuja, sun ki ba ta agajin gaggawa, har sai da jini ya gama zuba daga harbin da aka yi mata ta mutu.

An yi mamakin yadda aka ki karbar ta a asibiti, duk kuwa da cewa an kai ta na tare da wasu ‘yan sanda.

Nkechi dai kamar yadda ‘yar uwar ta Chinenye ta shaida wa PREMIUM TIMES, sun fita ne sun yi dinar murnar kammala aikin bautar kasa a Abuja.

Manyan jami’an asibiti a Abuja da Lagos da Ibadan da PREMIUM TIMES ta tuntuba, sun tabbatar da cewa asibitoci za su iya bayar da agajin gaggawa ga masu harbin binciga, ko da kuwa ba a kais u tare da jami’an tsaro ba.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta yi binciken wannan lamari.

Nkechi ta rasu a daidai lokacin da aka isa asibiti da ita. Vdama kuma an harbe ta ne wajen karfe uku na dare.

Share.

game da Author