Allah da lokaci ne kadai za su iya ganin bayan Buhari ba nPDP ba –Ndume

0

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa duk wata barazanar ‘yan sabuwar PDP ta barin jam’iyyar APC, ba za ta yi wani tasiri ba, domin Allah ne kadai da kuma lokaci ke yin komai.

Ndume ya na magana ne da manema labarai a Sakateriyar APC ta kasa a Abuja, inda ya kara da cewa, ita siyasa ra’ayi ce, kuma babu wani abin laifi idan wanda bai gamsu ba ya fito ya bayyana korafin sa.

Sai dai kuma ya kara da cewa duk wata fita da masu fita ke yi ko suke shirin yi, ba za ta shafi jam’iyyar APC a zaben 2019 ba.

Ya ce ya je ofishin jam’iyyar ne domin ya taya sabbin shugabanni murna.

“Ta ya za a yi tsammanin APC za ta gyara barnar da aka tabka a tsawonn shekaru 16, ita kuma ko shekara hudu ma ba ta yi ba?

“An gina wannan sakateriya a cikin shekaru biyu. A misali idan aka tashi, cikin miti 30 za a iya rusa ta.” Inji Ndume.

Share.

game da Author