Abin da ya sa na ki bin umarnin kotu na ki sauka daga kujerar Sanata –Aidoko Ali

0

Sanata mai wakiltar Kogi ta Gabas, Atai Aidoko Ali, ya ce shi ba zai sauka daga kujerar Sanata ba, har sai an yanke hukuncin karar da ya daukaka tukunna.

A cikin watan Yuni ne Babbar Kotun Tarayya, ta tsige shi daga kujerar Sanata.

Kallo ya koma sama a jiya Laraba lokacin da Sanata Aidoko ya bayyana a zauren zaman Majalisar Dattawa bayan da aka dawo daga hutu.

Sanatan ya ce ai tunda kotun da ya daukaka kara ta tsaida tsigewar da aka yi masa, bai ga dalilin da zai fasa zuwa majalisa ba, don haka har yanzu shi sanata ne.

Mai Shari’a Gabriel Kolawole ne ya tsige shi a cikin watan Yuni, a bisa hujjar kotun cewa ba shi ne ya cancanci zama dan takarar sanata a karkashin jam’iyyar PDP a shiyyar Kogi ta Gabas ba.

Mai adawa da Aidoko, mai suna Isaac Alfa ne ya kai kara cewa shi ne ya cancanta ba Aidoko ba. Wannan ne ya haifar da kakuduba tun bayan zaben fidda gwanin Sanatoci da PDP ta yi a cikin Disamba, 2014.

Share.

game da Author