Gwamnatin APC gwamnatin dabbobi ce -Inji Fayose

0

Gwamnan Jihar Ekiti mai barin gado, Ayo Fayose, ya bayyana gwamnatin APC da cewa gwamnati ce mai mulki tamkar na dabbobi.

Fayose ya yi wannan kakkausar furuci ne a lokacin da ya kai jaje ga Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Mataimakin sa Ike Ekweremadu bisa ga mamaya da shingen da jami’an tsaro suka yi musu a jiya Talata.

Da ya ke magana, Fayose wanda ya kai ziyarar a Majalisa, ya jinjina wa Sanatocin kasar nan bisa abin da ya kira jajircewar da suka yi wajen kare dimokradiyya daga masu yi mata hawan-kawara.

“Wannan ai mulkin dabbobi ne, domin dabba ita ce ke lalatawa ko ruguje abu. Ba ta da wani alfanu ga al’umma.

“Da a ce PDP ta yi irin wannan haukan a 2015, ai da su yanzu ba su hau kan mulkin ba.

“Tun a zaben da suka ce wai sun kayar da mu a Ekiti suka nuna cewa ko da karfin tsiya so suke su dawwama a kan mulki. Mu kuwa mu na da shaidar cewa ba a kayar da mu ba.” inji Fayose.

A karshe ya kara wa sanatocin kwarin-guiwar cewa su ci gaba da jajircewa, kada su bada kai bori ya hau.

Share.

game da Author