Kafa jam’iyyu ba shi da wani alheri a Najeriya -Tsohon Gwamna Attah

0

Tsohon Gwamnan Jihar Jihar Akwa Ibom, Victor Attah, ya bayyana cewa shi dai har yanzu bai ga wani abin alherin da jam’iyyun siyasa da aka kafa suka tsinana wa Najeriya ba.

Da ake tattaunawa da shi a wani gidan radiyo mai zaman kan sa, 105.9 FM a Uyo, babban birnin jihar, Attah wanda da shi aka kafa jam’iyyar PDP, ya ce idan an tuna lokacin mulkin Babangida ya kafa kwamitin tsara fasalin siyasar Najeriya.

“Ina cikin wancan kwamiti a lokacin, kuma ni a rahoto na, cewa na yi a soke tsarin jam’iyya, duk mai son fitowa takara ya fito shi kadai indifenda.

“Na bada shawara cewa ‘yan takara su tsaya a yi zaben kai da halin ka. Idan aka zabe ka ka yi wa jama’a abin kirki, sai a sake zaben ka. Idan kuwa ba ka yi komai ba, sai a zabi wani.

Attah, wanda ya yi ritaya daga shiga harkokin siyasa tun a 2015, ya koka da yadda ‘yan siyasa ke yawan tsilla-tsillar canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

Share.

game da Author