Rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wata budurwa mai suna Dorcas Adilewa ‘yar shekara 19 da aka kama da laifin saka wa a yi garkuwa da mahaifin ta.
Kwamishinan ‘yan sandar jihar Imohimi Edgal ya fadi haka ne wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litini a Legas.
Edgal ya bayyana cewa Dorcas ta shirya da wani saurayin ta mai suna Ifeoluwa Ogunbanjo da ya sace ta domin su damfari mahaifin ta kudi har naira Naira 600,000.
” Mun sami nasarar kama Dorcas da saurayin ta Ogunbanjo ranar 13 ga watan Yuli bayan mahaifinta ya shigar da kara a ofishin mu dake Ketu cewa wani ya kira shi da lambar waya mai kamar haka 09057432362 cewa wai sun sace ‘yar sa sannan suna bukatar sa ya biya Naira 600,000 kafin a sake ta.
” Jin haka sai muka fara bincike inda muka gano mabuyar wadannan masu garkuwa da Dorcas a Ijebu-Igbo jihar Ogun.
” Ranar 11 ga watan Yuli sai muka shirya farautar wadannan mutane a jihar Ogun inda bayan kwana daya muna neman su sai muka gano cewa barayin sun canza mabuya zuwa unguwar Ikotun dake jihar Legas.
” Da dai barayin suka ga babu mafita sai Dorcas ta kira mahaifin ta ta fada masa cewa masu garkuwan sun sake ta amma sai dai kafin wannan lokaci mahaifin nata ya fara tura musu kudi naira 8,000.
Edgal yace Dorcas ta tabbatar musu cewa itace ta shirya da saurayin ta a sace ta domin su karbi Naira 600,000 daga wajen mahaifin ta.
Ya ce a yanzu haka saurayin Dorcas da ita Dorcas tsare a ofishin su, sai bayan an kammala bincike a kai.