Shugaban hukumar kula da gidajen yari na Najeriya reshen jihar Neja Mustapha Iliyasu ya bayyana cewa hukumar su ta kamo fursinoni 51 daga cikin 210 da suka gudu daga kurkukun Minna jihar Neja.
Idan ba a manta ba a ranar 3 ga watan Yuni ne wasu fursinoni 210 suka gudu daga wannan gidan yari da taimakon wasu mahara da suka far wa gidan sannan ma har mutane biyu sun rasu a harin.
Iliyasu ya sanar da haka ne ranar Laraba da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna.
Ya ce sun hada guiwa ne da sauran jami’an tsaro a jihar har suka sami nasarar kamo wadannan fursinoni 51 cikin wadanda suka gudu.
Ya kuma kara da cewa har yanzu jami’an hukumar na farautar sauran fursinonin sannan yace sun dauki matakai da za su taimaka wurin hana sake faruwan hakan nan gaba.
” Muna kira ga mutane da su taimaka mana da duk bayanan da za su iya taimakawa dashi wajen kamo sauran fursinonin da muke farauta.”