Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar cewa mutanen uku sun rasa rayukan su sanadiyyar harin da aka yi a wasu kauyuka biyu a jihar.
Kakakin rundunar Mohammed Shehu ya sanar da haka wa manema labarai sannan ya bayyana cewa maharan sun far wa kauyukan Sikida da Gyaddu dake karamar hukumar Maradun ranar Laraba.
Shehu ya ce maharan sun tsere cikin daji bayan sun sami labarin cewa ‘yan sanda da sojoji na zuwa garin.
Bayan haka Shehu ya kuma kara da cewa ranar Talata dakarun ‘yan sanda sun yi arangama da wasu barayin shanu a kauyen Dangebe dake karamar hukumar Zurmi.
Ya ce maharan sun far wa kauyen da karfe takwas da rabi na safe.
” Sanadiyyar arangamar da muka yi da su ne ya sa suka gudu cikin daji sannan da dama cikinsu sun gudu da raunin harsashi a jikkunan su’’.
A karshe yace sun sami nasaran kwato shanu 171 sannan jami’an tsaro sun fara farautar wadannan mahara a cikin dajin da suka arce ciki.