An wayi gari ranar Laraba ne aka ga wasu sabbin ajujuwa da sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma Dino Melaye ya gina da zai kaddamar ranar Alhamis a kone kurumus.
Bayanai da suka iske mu, har yau ba a san ko su wane suka banka musu wuta suka kone kurmus ba.
Melaye ya gina ajujuwan guda biyu ne a Makarantar Sakandare ta Sarkin Noma, da ke Lokoja.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan labarin dai an kasa samun Dino Melaye domin jin ta bakin sa.
Ita ma lambar jami’in sa Gideon Ayodele a kashe ta ke.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Janga, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun samu labarin banka wa ajujuwan wuta, amma har zuwa yanzu ba a kai ga damke kowa ba tukunna.
Ya ce an bi dare ne an banka wutar aka sulale, shi ya kawo jinkirin saurin kama wadanda suka yi ta’asar.

