Kira ga gwamnati da ta samar da maganin rigakafin cutar Hepatitis da ke kama hanta

0

Wasu likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan Moses Adewumi da Femi Akinyode sun bayyana cewa mutane da dama a Najeriya basu da masaniya game wace irin cuta ce cutar Hepatitis, hanyoyin kamuwa da cutar da kuma hanyoyiin da za a iya bi domin nisan ta kai daga kamuwa da cutar.

Likitocin sun ce binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa cutar ta kashe mutane akalla miliyan 1.32 a duniya.

A Najeriya mutane miliyan 20 zuwa 30 na dauke da cutar sannan da dama ba su da masaniyyar matsayinsu game da cutar.

PREMIUM TIMES ta gana da wata matashiyar yarinya mai suna Tosan inda ta bayyana cewa yayayn ta ne ya tilasata mata yin gwajin cutar in ba haka ba bata san tana dauke da cutar ba.

PREMIUM TIMES ta zagaya wasu cibiyoyin kiwon lafiyar dake Abuja domin samun bayanai game da rigakafi da magungunar cutar.

Bayanan da ta samu daga cibiyoyin kiwon lafiyar da ta ziyarta ya matukar bata mamaki.

” Yara kawai muke yi wa rigakafi a nan banda manya. Amma idan kun je manyan asibitocin gwamnati da na kudi za ku iya samu.” Wani ma’aikacin cibiyar kiwon lafiya Byazhin a Abuja.

A asibitin Kuchingoro ma jami’an asibitin sun sahida mana cewa basu da maganin cutar a asibitin amma duk mai bukata zai iya samu a asibitin Jabi da wanda ke Wuse.

Da aka garzaya asibitin Jabi wani ma’aikacin fannin bada magani ya fada wa PREMIUM TIMES cewa suna yin allurar ne kan Naira 700.

” Muna fara aiki daga karfe 9 zuwa 12 na rana sannan mutum zai iya yin gwaji a wurin mu ko kuma a wani wuri sannan zai iya fara karban rigakafin a wurin mu ya karisa a wani wuri.

Ya ce sau uku ne suke yin allurar rigakafin cutar ga duk wanda bai dauke da cutar.

A asibitin Wuse kuwa ma’aikacin asibitin ya fada musu cewa suna yin allurar rigakafin cutar idan mutum ya biya Naira 500.

A karshe Moses Adewumi da Femi Akinyode sun ce kamata ya yi gwamnati ta samar da maganin rigakafin cutar domin kowa da kowa da kuma wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyon samun kariya daga kamuwa da ita.

Sun ce hakan zai taimaka wurin dakile yaduwar cutar musamman yadda cutar ke ganiyar yaduwa a kasan.

Share.

game da Author