A daren Asabar ne tsoffin gwamnonin jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Ibrahim Shekarau suka yi ganawar sirri a gidan Ibrahim Shekarau dake Abuja.
Ko da yake ba a fitar da bayanan abubuwan da suka tattauna ba, hakan dai yana da nasaba ne da dawowar kwankwaso jam’iyyar PDP daga APC.
Wannan ganawa dai shine ta farko a tsakanin ‘yan siyasan biyu tun 2011 sannan kuma ganawar na daga cikin shiri na farko kafin Kwankwaso ya gana da jiga-jigan jam’iyyar PDP.
Sai dai kuma akwai sauran rina a kaba domin kuwa suma fadar shugaban kasa sun wasa takubban su suna suna lallabar Shekarau ya dawo jam’iyyar APC daga PDP.
Bayanai sun nuna cewa gaba daya hankalin gwamnatin APC tun daga jiha zuwa sama, ya karkata ne zuwa nemo duk wata hanya da za a aiya bi a samu amincewar Shekarau ya dawo jam’iyyar APC daga PDP.