2019: Buhari ya umarci magoya bayan sa su jira INEC ta kada gangar kamfe tukunna

0

Fadar Shugaban Kasa ta fitar da sanarwa cewa ta na shawartar magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari da su jira har lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta hura usur kafin a fara kamfen.

Dokar INEC ta sahale wa ‘yan takara cewa sai ana saura watanni hudu zabe sannan za su fara takara.

Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Femi Adeshina ne ya fitar da wannan bayani, cewa “An lura magoya baya sun fara wasu abubuwa da za a iya fassarawa da cewa kamfen ne, ta hanyar wasu bayanai da talloli a jaridu kafafen yada labarai.”

“Yayin da ba wani laifi ba ne idan ana zakulo wasu muhimman ayyukan ci gaban da Shugaba Buhari ya aiwatar, to amma ya rika wuce gona da iri har ana kamfen, to wannan tsallen-Badake ne.’’

Daga nan sanarwar ta gode wa magoya baya, sannan ta ba su hakuri da su kai zuciya da kauna nesa, su hakura su jira har lokacin da aka amince a fara kamfen ya yi tukunna.

Share.

game da Author