Hukumar kare hakkin ‘dan Adam ta kasa (NHRC) ta bayyana cewa za ta hukunta duk wanda aka kama da laifin cin zalin mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra dake fadin kasar nan.
Shugaban hukumar Tony Ojukwu ya fadi haka a zaman da hukumar ta yi da jami’an tsaron a Yola jihar Adamawa ranar Alhamis.
Ojukwu yace za su gudanar da bincike domin gano masu aikata irin wadannan ayyuka na cin zalin mazauna sansanoninyan good dun hijra.
Ya ce za nemi ji daga bakin ma’aikatan jinkai dake kula da sansanonin ‘yan gudun hijira a sansanoin kasar nan.
” Za mu hukunta duk wanda muka kama da laifin hana ‘yan gudun hijira kayan tallafi da ake samar musu kamar abinci, magani, da sauran su.
Bayan haka Ojukwu ya jinjinawa rundunar ‘yan sandar kasar nan kan yadda suke kokarin ganin sun dakile irin wadannan matsaloli.
A karshe Ojukwu yace binciken zai taimaka wurin tsaro hanyoyin inganta aiyukkan ma’aikatan jinkai da sauran jami’an tsaron da ke aiki a sansanonin kasar nan.