Ficewar Kwankwaso daga APC bai dada ni da kasa ba – Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ficewar tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso ba t ta tada wa kowa hankali a jihar Kano ba, hasali ma mutane murna suka yi ta yi.

” Ficewar sa da sauran wadanda suka fice daga jam’iyyar APC ba bai dada mu da kasa ba, ina so in sanar wa mutane cewa su bude idanuwar su suga yadda za muyi da su a lokacin zabe.

Ganduje ya kwarmata wa a manema labarai haka ne a hira da yayi da su a Kano ranar Juma’a.

” Ina so ku zo Kano ku gani ko akwai wani abu da ake yi wai don Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar APC, kowa na ci gaba da hidimomin sa ne kawai kamar ma ba aji ba.

” Dama can Kwankwaso na so yayi takarar shgaban kasa ne amma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba sai ya fice daga jam’iyyar sannan Ina so in tabbatar muku cewa jihar Kano za ta ba Buhari kuri’un da bata taba bashi ba a zaben 2019.

Idan ba a manta Sanatoci 15 ne suka yi fitar burtu suka tsallaka zuwa jam’iyyar PDP.

Share.

game da Author