SUNAYE: Hadiman da Buhari ya nada wa matar sa da uwargidan mataimakin sa

0

Duk da alkawarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa idan ya zama shugaba zai soke ofishin matar shugaban kasa, sai ga shi cikakkun bayanai sun tabbatar da cewa Buhari ya karya wadannan alkarurra da ya yi.

Cikin wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust cikin Disamba, 2014, Buhari ya ce bai ga amfanin ofishin ba.

Maimakon haka, ya ce gara ma a karfafa ofishin Ministar Harkokin Mata sosai da sosai.

Wannan alkawari da Buhari ya yi, ya janyo masa farin jini sosai, musamman wajen zaben 2015, saboda a lokacin Patience Jonathan ta janyo wa ofishin bakin jini.

Sai dai kuma wani rahoto daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya tabbatar da cewa daga cikin Manyan Hadimai da Manyan mashawarta 118 da Buhari ya dauka, akwai ma’aikatan ofishin Uwargidan Shugaba da na ofishin Uwargidan Mataimakin Shugaba har su 10.

Ranar 1 Yuni, 2015 an nada Abiodun Adelowo a matsayin Likitar Matar Mataimakin Shugaban Kasa.

Sauran da aka nada a ofishin sun hada da Hadima kan Ayyuka na Musamman mai suna Tayo Basirat.

Akwai kuma Susan Chagwa Hadimar Harkokin Tsakar Gida da Harkokin Shirya Taro.

Sai Koko Iyamu Hadima kan Ayyukan Ofis da kuma Olasetikan Hadima kan Al’amurran Ofishin na Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa.

A Ofishin Uwargidan Shugaba Buhari kuwa, an nada Hajjo Sani a Bangaren Gudanarwar Aikace-aikacen ofis.

An kuma nada Mohammed Kamal Abdullahi a matsayin Likitan Uwargidan Shugaban Kasa. An nada mai suna Hauwa Uba Hadima ta Biyu a Ayyukan Ofis da Gudanarwa.

Sai dai kuma bincike ya tabbatar da cewa Susan Chagwa ta yi murabus, ba a sani ba ko bayan nan an nada wata ko ba a nada ta ba.

Dukkan nade-naden nan a cikin sirri aka yi su, ba a bayyanawa kamar yadda Buhari ya saba bayyana sunayen ma’aikata ko hadiman sa.

Lauya Femi Falana ya ce ofishin Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa haramtacce ne, domin babu shi a cikin sassa 320 na kundin tsarin mulkin Kasar nan.

Share.

game da Author