Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa ma’aikatar kiwon lafiya ta ware kashi 64 bisa 100 daga cikin kasafin kudin ta na 2018 domin ayyukan cibiyoyin kiwon lafiya da ke kasar nan.
Ya ce wannan mataki da ma’aikatar ta dauka ya nuna kokarin da wannan gwamnati ke yi na ganin ta samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga mutanen kasar nan.
Ya kuma kara da cewa yin haka ya zama dole ganin cewa cibiyoyin kiwon lafiya a kasar nan sune mutane suka fi ziyarta fiye da manyan asibitoci a kasar nan.
” A shekarun baya mun dauki matakin bunkasa asibitocin koyarwa a kasar nan domin samar da ingantaciyyar kiwon lafiya amma sai muka gano cewa talaka da ke zaune a kauye baya iya zuwa wadannan asibitocin.
” A dalilin haka muka amince mu bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar kara musu kason kudaden da suke samu daga kashi 18 zuwa 64 bisa 100 domin inganta kiwon lafiya a kasar.