Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta aika da sammacin a gaggauata sakin Sambo Dasuki. Ta aika sammacin ne ga Babban daraktan SSS da ake kira DSS da kuma Antoni Janar na Najeriya, Abubakar Malami.
A jiya Talata ne dai Dasuki ya cika sharuddan belin sa da kotun ta bayar tun a ranar 2 Ga Yuli.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa jiya ne da misalin karfe daya na rana, mutane biyu da suka tsaya belin Dasuki tare da jami’in bada beli na kotu, suka dunguma suka kai wa SSS da kuma Ministan Shari’a sammacin sanarwar a saki Dasuki.
Duk da cewa masu karbar belin sun yi tsammanin cewa za a damka musu Dasuki, majiya ta ce sai Darakatan SSS ya nemi iznin sakin sa daga fadar shugaban kasa tukunna.
Sau takwas kotu na bada belin Dasuki, kuma sauk bakwai kotu na kin bada belin sa.
Tun jiya ‘yan uwa da abokan arzikin Dasuki suka cika gidan sa su na jiran isowar sa.
Discussion about this post