Jami’an tsaro na cin zarafi na da na mukarrabai na, inji Gwamna Ayo Fayose

0

Gwamnan Jihar Ekiti mai barin gado, Ayo Fayose, ya koka ga babban basaraken Ado Ekiti, Ewi na Ado, inda ya nuna damuwa kan yadda jami’an tsaro suka kulle gidan gwamnati kafin zabe da kuma bayan zaben gwamna da ka gudanar ranar Asabar da ta gudana.

Fayose ya bayyana a karo na farko a Ado Ekiti, tun bayan kayar da jam’iyyar PDP zabe da aka yi ranar Asabar.

Ya ce har yanzu an cire masa jami’an tsaro, kuma iyalan sa na fuskantar musgunawa.

A lokacin da ya ke tafiya a kasa zuwa fadar basaraken, jama’a sun rika bin sa suna jinjina masa.

“Ran Sarki ya dade, na zo fada ne domin na sanar da kai cewa a ranar 14 Ga Yuli, ‘yan sanda sun mamaye Gidan Gwamnati tare da jami’an SSS, daga nan aka yin magudin zabe.”

“An kama sama da magoya bayan mu 300, ciki har da manyan jami’an gwmnati da dama. Hatta ana kusa da zabe, sai da aka yi gaganiyar minti 45 da mata ta a kofa, kafin jami’an tsaro su bar ta ta shiga cikin Gidan Gwamnati.”

“Tun daga zabe har yanzu an janye min jami’an tsaro, kuma gidan gwamnati ya na kulle.

“To zabe dai ya wuce, kuma dokar kasa ta ce ni ne dai gwamna har sai ranar 16 Ga Yuli, da wa’adi na zain kare. Ina sanar wa Sarki da dukkan duniya cewa har yanzu ba ni da walwala a gidan gwamnati.

“Ina so ka fada wa duniya cewa an ba wanda ya yi takara da mu jami’an tsaro, ni kuma an janye nawa. Ka fada wa gwamnatin tarayya da kuma shugaban ‘yan sanda da duniya baki daya.

A na sa jawabn, basaraken ya gode wa Allah da ya tserad da Fayose da ran sa a lokacin zabe.

Ya ce bai ji dadin abin da ya faru ba, musamman yadda ya ga gwamnan ya je fadar sa a cikin bakaken kaya, to ya san akwai damuwa da matsala, tun a ta su al’ada ba a sa bakaken kaya, sai idan wani mummunan abu ya afku.

Ya ce zai mika kudaden sa ga Majalisar Masarautar Jihar Ekiti, kuma ya na rokon jami’an tsaro da su maida wa Fayose masu tsare da lafiyar sa.

Fayose zai fuskanci tuhuma – EFCC

A wata sabuwa kuma, Hukumar EFCC, ta bayyana cewa gwamna mai baring ado na jam’iyyar PDP a jihar Ekiti, Ayo Fayose, zai fuskanci tuhuma da ya kammala wa’adin sa daga kujerar gwamnan jihar.

Jim kadan bayan bayyana zaben jihar Ekiti, wanda dan takarar APC ya yi nasara, EFCC ta buga wani shagube da gugar-zana a kan Fayose cewa, za ta kakkabe wani fayil na wata harkallar da ake zargin ya tafka wajen gina wani gidan kaji na naira biliyan 1.2

Sai dai kuma ganin yadda dimbin jama’a suka rika watsa wa EFCC yawun tofin Allah-tsine da zargin cewa hukumar ta koma amshin-Shatan ‘yan siyasa, sai EFCC ta yi sauri ta cire bayanin da ta buga din game da Fayose.

Shi ma kakakin Fayose, Lere Olayinka, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa abin da EFCC ta tura a shafin tweeter rashin mutunci ne. ya na mai cewa idanun EFCC ya rufe, har ta manta cewa ita fa hukumar ba kotu ba ce, amma ta ke kokarin yanke hukunci tun ma kafin a je kotun.

“Ayo Fayose dai har yau shi ne gwamna, sai su jira har 16 Ga Oktoba, tukunna.”

Sai dai kuma, a cikin wani jawabi da EFCC ta tura wa PREMIUM TIMES, ta bayyana cewa kotu ce kadai za ta iya wanke Fayose da ya sauka gwamnan jihar Ekiti.

Haka kakakin hukumar Wilson Ewujeran ya shaida.

Share.

game da Author