Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya bada karin dangane da shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar APC.
Da ya ke magana wurin nada Babban Mai Bada Shawara kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Jerome Torshimbe, Otom ya kara da cewa jam’iyyar APC ta ba shi “jan kati”.
Kakakin yada labaran gwamnan, Tahav Agergua ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan labari.
“Batun jam’iyya zan iya cewa an ba ni jan kati kuma ba na cikin filin kwallon jam’iyyar. Kenan tunda an daga min jan kati, har na fice daga cikin filin, na zama mai zaman kai na kenan.”
“Amma dai ban san abin da zai faru ba nan gaba, amma dai ina zaman jira tukunna.
Ya ce zai shaida wa al’ummar jihar Benue idan wata kungiyar kwallon kafar zai koma.
Discussion about this post