An damke Dagacin Atibe kan zargin yin garkuwa da ma’aikatan hakar mai 19

0

Kallo ya koma sama, yayin da rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta damke Dagacin kauyen Atiba, bisa laifin hada baki da shi a saci ma’aikatan kamfanin hako danyen mai na Exxon Mobil su 19.

Kakakin ‘yan sandan jihar MacDON Achebe ya tabbatar da haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Karamar Hukumar Eket da ke jihar Akwa Ibom.

“Da farko dai mutane hudu da suka yi garkuwar ne aka fara kamawa, amma sai suka ce ai Dagacin yankin ne ya sahale musu cewa su je su sace mutanen.” Haka Achebe ya furta.

Dagacin mai suna Inam Unanaowo, an ce ya bada umarnin sace ma’aikatan ne saboda kamfanin bai dauke su aiki ba.

Kakakin na jami’an ‘yan sanda ya ce da an kammala bincke za a maka su kotu.

Share.

game da Author