Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta bayyana cewa Najeriya ta yi asarar kimanin naira bilyan 7.157 sanadiyyar hadurran da suka rika da motocin dakon man fetur guda 116 a cikin watanni shida, watau makonni 25, ko kuma a ce rabin shakara daya na shekarar 2018.
Shugaban Hukumar na Kasa, Boboye Oyeyemi ne ya bayyana haka a wani taron wadanda ke da hannu a harkokin sufurin motocin dakon man fetur a ranar Litinin a Abuja.
Oyeyemi yace wannan asara ta dukiya ce kadai zunzurutun ta, babu lisafin wadanda suka rasa rayuka tukunna.
Ya kara da cewa adadin ba ya kuma dauke da kudaden da wadanda suka ji raunuka ke kashewa a asibiti, ko damejin da ake yi wa titi idan an yi hadari.
Ya kara da cewa a hadari ranar 28 Ga Yuni da tankar daukar fetur ta yi a Gadar Otedola, ya haddasa asarar rayuka 12, kuma motoci har 55 sun kone kurmus. Ya dora laifukan hadurran a kan rashin kiyaye bin ka’idojin titi ko tuki.