Hukumar NYSC ta ce satifiket din Minista Kemi na bogi ne sai dai…

0

Hukumar Kula da Ayyukan Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), ta nesanta kanta da satifiket din dauke wa Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ke ikirarin cewa hukumar ce ta ba ta.

NYSC ta yi haka ne a matsayin martanin labarin da PREMIUM TIMES ta buga inda ta zargi Adeosun da mallakar takardar NYSC ta bogi.

Labarin dai ya tada kura, har dimbin jama’a da dama suka rika yin kiraye-kirayen Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta umartar ta da ta yi murabus daga mukamin ta.

Jami’ar Yada Labarai ta Hukumar NYSC mai suna Adenke Adeyemi, ta rubuto wa PREMIUM TIMES wasika ta e-mail, inda ta tabbatar da cewa tabbas Kemi ta taba rubuto wasikar neman katin shaidar sahale mata yin aikin bautar kasa, bisa ga dalili na yawan shekarun ta sunn zarce na wadanda aka wajibta wa suka aikin bautar kasa.

Sai da kuma ta kara cewa za a binckika a gano ta yadda aka yi ta mallaki wannan katin na jabu.

PREMIUM TIMES ta ba da labarin yadda Majalisar Dattawa da ta Tarayya suka rika maida Kemi saniyar-tatsar biliyoyin nairori.

Ta rika biya musu bukatar su ko da kuwa Shugaba Muhammadu Buhari bai amince ba, ko bai sa hannu ba tukunna.

Yanzu dai ‘yan Najeriya sun zura wa Shugaba Buhari ido a gaya zai yi da Kemi. Za ta sauka ne? Zai tsige ta? Ko kuma zai yi mirsisi kamar yadda ya yi mirsisi wajen kin hukunta Babachir Lawal da kuma jami’an gwamnatin sa da suka yi sunkurun maida Abdulrashid Maina a kan aikin sa?

Share.

game da Author