RASHA 2018: Japan ta doke Columbia 2-1, bayan an ba dan wasa jan kati

0

Kasar Japan ta yi nasara a kan Columbia, bayan da alkalin wasa ya bai wa Carlos Sanchez jan kati minti biyu kacal da fara wasa.

Japan ta jefa kwallaye biyu yayin da Columbia ta ci kwallo daya.

An bai wa Carlos jan kati a daidai minti na biyu, wanda hakan ya sa ya ajiye tarihi cewa shi ne aka ba jan kati cikin kankanen lokaci a wasan na Rasha, kuma ta tarihin wasan cin kofin duniya, shi ne na biyu wajen saurin karbar jan kati daga fara wasa.

Sun fafata wasan ne a filin wasa na birnin Mordovia, Rasha.

Ya samu jan kati ne a daidai lokacin da ya sa damtsen hannun sa ya tare wata kwallo da fitaccen dan wasan Japan, Shinji Kagawa ya buga a daidai minti na 2:56 da fara wasa.

Kagawa din ne kuma ya jefa kwallon a ragar Columbia a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

An dai tashi wasan 2-1.

Share.

game da Author