Hukumar Kwallon Kafa ta Saudiyya ta bayyana cewa ‘yan wasan ta sunn isa birnin Rostov na kasar Rasha lafiya, bayan da jirgin da ke dauke da su ya samu matsaar inji a lokacin da ya ke a sararin samniya.
Mahukuntan hukumar kwallon sun ce matsalar ba babba b ace, amma dai daya daga cikin injinan jirgin ne ya samu matsala
Wani faifan bidiyo da aka watsa a soshiyal midiya ya nuna hoton jirgin daidai lokacin da bangaren fukafikin sa daya ke cin wuta a lokacin da ya ke shawagi a sararin sama.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN, Reuters da PREMIUM TIMES ne suka ruwaito labarin.