Dandazon masu zanga-zanga sun zagaye hedikwatar ofishn jam’iyyar APC na kasa da ke Abuja.
Hedikwatar, wadda ke kan hanyar zuwa Barcelona Hotel, ta na kusa da otal din Valencia ne a Wuse II, Abuja.
Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalayen da ke kunshe da rubutun neman a yi waje-rod da shugabannin da ke kai na yanzu, karkashin shugabancin John Oyegun, wadanda aka yi niyyar saukewa idan an zo gangamin jam’iyyar na kasa a ranar Asabar mai zuwa.
Har ila yau kuma, su masu zanga-zangar, su na kuma dauke da kwalayen da ke nuna jinjina ga babban dan takarar shugabancin jam’iyya daya tilo, Adams Oshimhole.
Wa’adin su Oyegun dai zai kare ne a ranar Asabar mai zuwa idan an zo taron gangamin jam’iyya, domin a ranar ce za a zabi sabbi shugabannin jam’iyyar APC.