KASAFIN 2018: Majalisar Tarayya sun bayyana dalilin su na kara kasafin su zuwa naira bilyan 139.5

0

Mambobin Majalisar Tarayya sun kare dalilin su na yi wa kasafin majalisa karin kudi daga naira bilyan 125 zuwa naira biyan 139.5.

A bayanan su, sun bayyana cewa kasafin su ya yi karanci sosai, idan aka yi la’akari da na shekarun baya.

Sai dai kuma sunn kasa bayar da wata gamsasshiyar hujjar yin wawakeken karin makudan kudaden da suka yi.

Buhari ya zarge su da yin azuzurun kudade a kasafin su, kuma sun bi kasafin dalla-dalla su na zaftare kudade, har ta kai ga ya ce da wuya ma wasu muhimman ayyukan da aka yi kudirin aiwatarwa su tabbata.

Kakakin Majalisar Tarayya, Abdulrazak Namdas, ya fitar da bayanin cewa kasafin Majalisar Tarayya ko kusa bai kai na naira bilyan 150 da ake musu ba kafin shekarar 2015.

“Kafin 2015, ana ware wa Majalisa kasafin naira biliyan 150 a tsawon shekaru da dama. Amma a 2015 sai aka yanke shi ya koma naira biliyan 120. Cikin 2016 kuma sai aka kara zabtare shi ya koma naira biyan 115.

“Kasafin mu na 2017, naira biliyan 125 ne. Yanzu kuma na 2018, naira bilyan 139.5 ne. To kun ga har yanzu bai ma kai na naira biliyan 150 da ake yi masa kafin 2015 ba kenan.”

Daga nan majalisa ta ce ta na goyon bayan Buhari da a ja zaren aiki da kasafin kudi daga Janairu zuwa Disamba.

A kan haka, sun bayyana cewa a rika kai musu kasafi tun daga cikin watan Satumba su fara dubawa da wuri.

Shugaba Buhari ya yi korafin cewa majalisa ta rage har naira bilyan 347 daga cikin ayyuka 4,700 da aka kebe za a yi wa jama’a.

Ya kara da cewa su kuma sun saka ayyukan da suke so a yi a mazabun su guda 6,403, na kusan naira bilyan 578.

A kan wannan ne Namdas ya ce ya kamata jama’a su kula da cewa su fa jama’a suke wakilta, don haka sun saka ayyukan da za su amfani al’ummar da suke wakilta ne kai tsaye.

“Wasu ayyukan da ministoci suka cusa wa Buhari a cikin kasafin kudi, kwata-kwata ba su da wani tasiri ko muhimmancin kai tsaye ga talakawa.” Inji Mamdas.

Share.

game da Author