Shugaban hukumar kare hadurra na kasa (FRSC) reshen jihar Jigawa Angus Ibezim ya bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukan su sannan wasu hudu sun sami rauni sanadiyyar hadarin mota da aka yi a hanyar Hadejia zuwa Kaugama.
Ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba.
Hadarin ta auku ne yayin da tankar mai da wata mota mai kirar ‘Citroen’ suka yi karo gaba da gaba bayan direbobin basu ganin gaban su sabo ruwan sama da a ke yi kamar da bakin kwarya.
Ibezim ya ce sun tsinci tsabar kudi da ya kai Naira miliyan 1,216,870, wayar tarho shida da tufafi wanda za su mayar da su wa ‘yan uwan mutanen da suka yi hadari idan suka gama bincike.