Gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kebbi, Usman Dakingari, tare dawasu mutane uku a kotu, ta samu cikas, saboda ukun da ake tuhumar sa tare da su ba su bayyana a gaban mai shari’a ba.
Sauran ukun da ake tuhuma tare da Dakin gari, sun hada da Garba Kamba, Sunday Dogonyaro da kuma Abdullahi Yelwa.
An umarci mai gabatar da kara da ya gabatar da su a kotu jiya Laraba, amma ukun duk ba su bayyana ba, sai Garba Kamba kawai, wanda ya kai kan sa a ofishin hukumar na Kano, shi kadai ne aka gurfanar a gaban kotun.
Ana zargin su da karbar naira miliyan 700 daga cikin dala miliyan 115 da aka ce tsohuwar Ministar Fetur, Deizani Alison Madueke ta kassafa domin a yi barankyankyama ga sakamakon zaben 2015.
Lokacin da aka kira shari’ar a jiya Laraba, mai gabatar da kara, Johnson Ojogbane, ya bayyana wa kotu cewa ya yi hobbasa ba sau daya ko sau biyu ba, da nufin aika wa sauran wadanda ake tuhuma da sammaci, amma sai kulli-kurciya suke yi masa.
Daga nan sai mai gabatar da kara ya roki kotu da ta ba shi izni ko iko a karkashin doka ta 2015 ya mika sammacin kiran su ga lauyoyin su ko wadanda suka tsaya musu beli, ko ta hannun wani baligi da ke zaune a gidajen su, kai ko ma ta hanyar lika sammacin a kofar gidajen su.
Nan take Mai Shari’a ya bada umarnin cewa a aika musu da sammamci ga lauyoyin su ko wadanda suka tsaya musu beli, ko ta hannun wani baligi da ke zaune a gidajen su, kai ko ma ta hanyar lika sammacin a kofar gidajen su, kamar yadda mai gabatar da kara ya nemi izni.
Shi kuma Garba Kamba, kotu ta ce ya yi tafiyar sa gida, amma ya tabbatar da ya kai kan sa kotu a ranar da za a ci gaba da zaman shari’ar.
An daga karar zuwa ranar 25 Ga Yuni, 2018.
An kuma damka sammamcin Dakingari a gidan sa da ke unguwar GRA, Birnin Kebbi duk a jiya Laraba a minsalin karfe 1:51 na rana.
Wani mazaunin gidan mai suna Mohammed Danladi ne aka damka wa sammacin aka ce ya bai wa Dakingari, kuma ya sanar da shi cewa sammamacin na kunshe da neman sa da ake yi ya kai kan sa kotu tare da sauran wadanda ake tuhumar sa tare su uku, a ranar 25 Ga Yuni.
Discussion about this post