Babban mai kocin Super Eagles, Germot Rohr, ya bayyana cewa yawan tafka kura-kurai yayin da suke taka leda ne ya janyo kasar Croatia ta lallasa Najeriya da ci biyu da nema.
Da ya ke magana daga bayan kammala wasan ne ya ce ‘yan wasan Najeriya su na sane da cewa sun yi kura-kurai a wasu muhimman lokutan da bai kamata su yi kuskuren ba.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito daga birnin Kaliningrad inda a can ne rukunin D inda Najeriya da Croatia, Agentina da Iceland suke.
“Mu na sane cewa mun tafka wasu manyan kura-kurai, kuma a fili ta ke cewa tilas sai fa mun kara kokari idan mu na son tsira da mutuncin mu.
Kocin na Najeriya ya ce gaba dayan ‘yan wasan na sa ba su ji dadin yadda wasan ya karke ba.
Rohr ya yarda cewa kalubalen da ke gaban ‘yan Najeriya ya karu tunda kungiyar ta sha kashi.
Ya ce rawar da Mikel ya taka dama hakan suke so ya yi, kuma haka din ya ke yi tun farkon fra horas da ‘yan Najeriya da ya ke yi.
“Ya samu cikas ne saboda irin gogewa da kwarewar ‘yan wasan da muka fafata da su na kasar Croatia.